dcsimg

Sauro ( Hausa )

provided by wikipedia emerging languages

Sauro yanada kafofi hudu kuma yana da fuka-fukai biyu yana shi dabba ci irin wayanda tashe shima kawa howane halitu ne yanada mace da miji yana shan jinin mutun har yasamasa zazzaɓin cizon sauro na daya daga cikin cututtukan da suka fi yin kisa a duniya, inda ta ke kama miliyoyin mutane a kowace shekara. Yara fiye da miliyan daya suke mutuwa kowace shekara a sanadin wannan cuta da sauro ke yada ta. Abin tayar da hankali shi ne a yanzu an ga alamun cewa sauro ya fara jurewa magungunan kashe kwarin da ake yin amfani da su wajen kashe shi. Amma kuma a wani bincike da Daliban Jami'ar Kimiyya da fasaha ta jihar Kano dake Wudil, KUST, Wanda Al'amen Baba ke jagoranta sun gano wasu kwayoyin halitta a jikin sauron wadanda suke sanya shi jurewa wadannan magunguna.

Anopheles gambiae

Hilary Ranson ta Makarantar nazarin Cututtukan dake Addabar Kasashe Masu Zafi ta ce daya daga cikin muhimman makaman da ake yin amfani da su wajen hana yaduwar zazzabin cizon sauro shi ne ta yin amfani da gidan sauro. Amma kuma, tilas ne gidan sauron a ringa jika shi sau da dama cikin shekara guda da wani maganin kashe kwari, musamman magunguna dangin Pyrethroid.

Ranson ta ce, "wadannan magungunan kashe kwari sun samu nasara sosai wajen dakile zazzabin cizon sauro, amma a cikin 'yan shekarun nan mun ga sauron ya fara jure ma irinw adannan magunguna. Wannan kuwa ya dame mu sosai a saboda ba mu da wasu magungunan masu yawa da zasu iya maye gurbinsu."

Anopheles stephensi.jpeg

Ranson ta ce akwai wasu yankuna na Afirka inda ake samun karin sauro mai dauke da kwayar cutar maleriya dake jure magungunan kashe kwari dangin Pyrethroid. A saboda haka ne ita da wasu masana na kasa da kasa suka nemi sanin abinda ya sa sauron ya fara jurewa magungunan.

 src=
Mûn-é

Ta ce, "mun gano wasu ruwayen halitta guda biyu wadanda yawansu a jikin sauro mai jurewa magungunan ya zarce yadda yake a jikin sauron da ba ya iya jurewa. Haka kuma mun samu nasarar nuna cewa wadannan ruwayen halitta su na iya lalata magunguna kashe kwarin. Wannan shi ya sa sauron da yake dauke da wadannan ruwaye biyu yana iya narkarwa ya lalata magungunan kashe kwarin da suka taba jikinsa, ta yadda ba zasu iya yi masa komai ba balle su kashe shi."

Haka kuma Ranson da sauran masanan sun samu nasarar gano kwayar halittar dake samar da wadannan ruwaye a jikin sauron. Ta ce wannan abu ne mai matukar muhimmanci.

"A yanzu zamu iya yin sauyi ga maganin kwarin ta yadda zai iya kashe koda sauron dake da irin wadannan ruwayen. Hanyar da zamu bi mu yi haka kuwa, ita ce ta sauya sinadaran dake cikin magungunan domin canja fasalin aikinsu ta yadda a bayan kashe sauron, zasu kuma hana kwayayen halittar sauro sarrafa wadannan ruwaye. Ta yin haka, maganin zai jima sosai cikin kaifinsa a jikin kowane irin sauro. Wannan zai maido da kaifin magungunan."

Anson ta ce wannan bayanin zai taimaka wajen tabbatar da ci gaban makami mai kaifi da amfani a yakin da ake yi da zazzabin cizon sauro. An buga sakamakon wannan bincike nata a cikin mujallar nan mai suna "Genome Research".

Wurin da yake taruwa

Sauro yana taruwa a wurin zubda ruwa har yataru se matarsa ta shiga ciki dan tayi kwai kawa ruwa sama in ya taruw ko ruwan wanka in yataro

Anazarci

license
cc-by-sa-3.0
copyright
Masu marubutan Wikipedia da masu gyara

Sauro: Brief Summary ( Hausa )

provided by wikipedia emerging languages

Sauro yanada kafofi hudu kuma yana da fuka-fukai biyu yana shi dabba ci irin wayanda tashe shima kawa howane halitu ne yanada mace da miji yana shan jinin mutun har yasamasa zazzaɓin cizon sauro na daya daga cikin cututtukan da suka fi yin kisa a duniya, inda ta ke kama miliyoyin mutane a kowace shekara. Yara fiye da miliyan daya suke mutuwa kowace shekara a sanadin wannan cuta da sauro ke yada ta. Abin tayar da hankali shi ne a yanzu an ga alamun cewa sauro ya fara jurewa magungunan kashe kwarin da ake yin amfani da su wajen kashe shi. Amma kuma a wani bincike da Daliban Jami'ar Kimiyya da fasaha ta jihar Kano dake Wudil, KUST, Wanda Al'amen Baba ke jagoranta sun gano wasu kwayoyin halitta a jikin sauron wadanda suke sanya shi jurewa wadannan magunguna.

Anopheles gambiae

Hilary Ranson ta Makarantar nazarin Cututtukan dake Addabar Kasashe Masu Zafi ta ce daya daga cikin muhimman makaman da ake yin amfani da su wajen hana yaduwar zazzabin cizon sauro shi ne ta yin amfani da gidan sauro. Amma kuma, tilas ne gidan sauron a ringa jika shi sau da dama cikin shekara guda da wani maganin kashe kwari, musamman magunguna dangin Pyrethroid.

Ranson ta ce, "wadannan magungunan kashe kwari sun samu nasara sosai wajen dakile zazzabin cizon sauro, amma a cikin 'yan shekarun nan mun ga sauron ya fara jure ma irinw adannan magunguna. Wannan kuwa ya dame mu sosai a saboda ba mu da wasu magungunan masu yawa da zasu iya maye gurbinsu."

Anopheles stephensi.jpeg

Ranson ta ce akwai wasu yankuna na Afirka inda ake samun karin sauro mai dauke da kwayar cutar maleriya dake jure magungunan kashe kwari dangin Pyrethroid. A saboda haka ne ita da wasu masana na kasa da kasa suka nemi sanin abinda ya sa sauron ya fara jurewa magungunan.

 src= Mûn-é